'Atiku Abubakar ya samu nasara a mazaɓarsa'
Babban baturen zabe a mazaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar yace Atikun ya lashe zaɓe a rumfar da ya jefa ƙuri'a.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Atikun ya samu ƙuri'a 282 a rumfar.
Sauran jam'iyyun da suka samu ƙuri'a sun haɗa da;
APC - 57
LP - 6
AP - 2
NNPP - 1
Boot Party - 1