Rahoto kai-tsaye
Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar Labour Peter Obi, ya kaɗa kuri'arsa a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
'Yan jarida ne suka cika rumfar zaɓen dan takarar da ke Agulu, domin ɗaukar yadda Obi zai kaɗa kuri'ar.
Mista Obi, ana masa kallon shi ne mutum na uku mai tarin magoya baya da suke neman takarar shugabancin ƙasar.
Kamar sauran 'yan takarar Obi ma ya halarci wajen zaɓen tare da uwar gidansa.
Ɗan takara shugaban ƙasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa da ke ƙaramar hukumar Madobi a jihar Kano.
Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano na ɗaya daga cikin ƴan takarar shugabancin ƙasa da ake ganin za su taka rawar gani a zaɓen na 2023.
Ya fito ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe, inda ya kaɗa ƙuri'ar tasa.
Yayin da ake ci gaba da zaɓe a Najeriya, nan wasu 'yan gudun hijira ne suka yi dafifi domin kaɗa ƙuri'arsu a rumfar zaɓe da ke makarantar firamare ta Malkohi 009 a birnin Yola.
Rumfar zaɓen tana da mutum 1,228 da suka yi rajista domin yin zaɓe.
Sai dai, yawancinsu a wannan rumfar sun kasance ƴan gudun hijira ne.
"Na fito inyi zabe ne saboda in kawo gwamnati da za ta mayar da ni garina Gwoza, in ji Hadiza Abubakar, 'yar gudun hijira da ke zaɓe a rumfar zaɓen da 'yan gudun hijira ke kaɗa kuri'a na makarantar Malkohi a Yola.
Matar dai, mai shekara 40 ta kuma ce tana da yara 8. Ta ce ta bar Gwoza shekaru 8 da suka gabata.
Ta hau layin zaɓe tun karfe 7 na safe.
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙuri'arsa a mazaɓarsa ta Awolowo da ke Falomo da ke Legas.
Da misalin ƙarfe 9:30 na safe ne dan takarar ya isa inda zai ƙaɗa kuri'ar tasa tare da mai ɗakinsa Oluremi Tinubu.
An samu jinkiri gabanin fara kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓen, sai dai daga baya zaɓen ya kankama. Akwai mutum aƙalla 832 da suka yi rajistarsu a wannan rumfar zaɓe.
Yayin da harkokin zaɓe ke ci gaba da gudana a wasu sassan Najeriya lami lafiya, wasu ɓangarorin suna fama da matsaloli da dama.
Kama daga rashin isar jami'an INEC a kan lokaci zuwa na rashin tsaro kamar a abin da ya faru a jihar Gombe.
Sai dai matsalar da ake fsukanta a Maiduguri babban birnin Jihar Borno ta sha ban-ban da ta sauran jihohi.
A Maidugurin matsalar na'urarar tantance masu kaɗa ƙuri'a ita ce ta ƙi aiki yadda ya kamata.
Kazalika ana fuskantar rashin fitowar masu zaɓe kamar yadda mai turo wa BBC bayani daga Maiduguri, Adamu Aliyu Ngulde ya tabbatar wa BBC.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuria'a mazaɓarsa da ke garin Daura da ke jihar Katsina.
Shugaban wanda ya fito da misalin ƙarfe 9:30 na safe ya kaɗa ƙuri'ar tasa ne tare da mai ɗakinsa A'isha Buhari.
Muhammadu Buhari na kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas a wannan shekara, inda ake sa rana zai miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa an samu jinkirin kayan aiki a mazaɓar Madachi, a Kofar Fada da ke Ƙaramar hukumar Katagum.
A mazaɓar Shagari da ke tsakiyar Bauchi ita ma ana fuskantar wannan matsala ta rashin kai kayan aiki a kan lokaci.
Hakan abin yake a ƙofar gidan yari, kan kusurwar fada da sauran wasu wurare.
An fara kaɗa ƙuri'a a mazabar Iwo da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo.
Tun da sanyin safiya ne masu kaɗa ƙuri'a suka isa rumfunan zaɓen domin kaɗa kuri'unsu.
Yankin na cikin inda aka fara kaɗa kuri'a a kan lokaci a kusan faɗin Najeriya, ma'ana ba su samu jinkiri ba kamar yadda aka samu a wasu wurare da dama.
Tun da fari an raba layukan masu zaɓen biyu domin sauƙaƙe komi, Layin farko na dattijai da mata masu ciki da kuma masu buƙata ta musamman.
Layi na biyu kuma matasa ne masu jini a jika da kuma lafiyayyun mutane koda suna da shekaru.
Hukumar ICPC reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wani mutum ɗauke da kuɗi da suka kai naira miliyan biyu, ciki da sababbi da kuma tsofaffin kuɗin da aka sauya.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ta kama mutumin ne mai suna Hassan Ahmad da waɗannan kuɗaɗe duk da ƙaranci kuɗi da ake fama da shi.
"An kama shi da naira dubu ɗari tara na sababbin kudin da aka sauya, yayin da sauran naira miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya suka kasance na tsofaffin kuɗi.
"An shirya kuɗin ne cikin irin jakar nan ta buhu, kuma tuni mutumin ya amsa laifinsa ya na cewa kudin zai kai su jihar Gombe ne ga wani ɗan siyasa.
Rahotanni da ke fitowa daga mazaɓar Etoi a ƙaramar hukumar Uyo na cewa har yanzu ana jiran jami'an hukumar INEC su isa wuraren zaɓen.
Wannan ce dai mazaɓar da ɗan takarar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya kaɗa ƙuri'arsa a ciki.
Duk da cewa masu zaɓe sun isa runfunan tun ƙarfe shidan safe amma sun ce har yanzu ba su ga ko ma'aikacin INEC ɗaya da ya iso wajen aikin ba.
Akwai rumfunan zaɓe da BBC ta ziyarta a yankin, dukkansu suna fama da irin wannan matsalar suma.
Wasu ma'aikatan wucin-gadi na hukumar zaɓe a Najeriya sun ce ba za su fara aikin tantance masu kaɗa ƙuri'a ba har sai an biya su wasu alawus-alawus ɗinsu.
Ma'aikatan na Mazaɓar Ɗorayi Karama a Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar, sun ce suna neman alawus ne na horaswar da INEC ɗin ta ba su.
Wakilin BBC Hausa a Kano Zahradden Lawan ya ce yanzu haka masu zaɓe na can sun yi cirko-cirko suna jiran ikon Allah.
Jihar Kano na da masu kaɗa ƙuri'a fiye da miliyan biyar, abin da ya sa jihar ta zama ɗaya daga cikin wuraren da 'yan takara suka fi kewayawa domin neman ƙuri'u.
An fara kaɗa ƙuri'a a mazaɓa ta 019, gundumar Amatutu ta 2, a garin Agulu da ke jihar Anambra, inda nan ne rumfar zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Peter Obi.
Peter Nedum, mai shekara 81 shi ne mutum na farko da ya kaɗa ƙuri'arsa.
Duk da barazanar tsaro da ake fuskanta a yankin kudu-maso-gabashin Najeriya, da alama mutane da dama sun fito domin kaɗa ƙuri'a.
Jinkirin da aka samu na isowar jami'an INEC a mazabar Ajiya inda nan ne ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, zai kada kuri'asa, a jihar ta Adamawa ta sa an samu ɗan jinkiri wurin fara tantance masu kaɗa ƙuri'a.
Duk da cewa Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta ce za a fara zaɓen ne da ƙarfe 8:30 na safe, jami'an zaɓen ba su iso ba sai kimanin ƙarfe 8:15am.
Hakan ne ya sanya ba a samu nasarar fara tantance masu kaɗa ƙuri'ar a kan kari kamar yadda aka tsara ba.
Wasu da ake zargin ƴan bangar siyasa ne sun kai wa jam’ian zaɓe na wucin-gadi da aka tura wata rumfar zaɓe da ke cikin garin Gombe.
Rahotanni sun ce maharan ɗauke da sanduna da adduna sun ƙwace wa ma’aikatan wayoyi da jakkunansu da wasu kayan aiki.
Haka nan an garzaya da wasu daga cikin ma’aikatan zaɓen zuwa asibiti bayan sun samu raunuka.
Wakilin BBC Hausa na wucin-gadi a Gombe Halilu Mohammed Teli ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare kuma yawancin waɗanda aka kai wa farmakin matasa ne masu yi wa ƙasa hidima.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Gombe ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce sun kama wasu daga cikin maharan sannan sun fara gudanar da bincike kan abin da ya faru.
Salisu Atiku, mai shekara 19 na daga cikin na farko-farko da suka fito domin kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe ta Tukuntawa da ke jihar Kano.
Wannan ne karon farko da zai yi zaɓe, kuma ya ce ya ƙagu ya kaɗa ƙuri'arsa.
Ya ce "Magabatanmu na ba mu labarin yadda Najeriya take da daɗi a shekarun baya, abin da nake fata shi ne ƙasarmu ta koma kamar yadda take a baya, shi ya sa zan yi zaɓe."
Wannan shi ne Alase Adesina, wanda ya zama na farko a layin zaɓe a mazaɓar at St Agnes da ke Alagomeji a Mainland Legas.
Ya shaida wa BBC cewa ya fito ne domin ya zaɓi ra'ayinsa a wannan zaɓe, yana kuma jin kishin ƙasarsa a kan hakan.
"Ina cikin farin ciki matuka, ina jin daɗi kuma yanzu ina jira in jefa kuri'ata ne kawai. Ina kuma fatan kada a yi mana maguɗi."
Ya shafe sama da minti 30 yana jira gabanin a fara batun zuwan sauran mutane har a zo maganar kaɗa kuri'a.