Messi zai koma Newell Old Boys, Brazil za ta dauki Enrique
Kyaftin din Argentina, mai taka leda a St-Germain, Lionel Messi na duba yiwuwar komawar Newell Old Boys, wadda ya fara yi wa tamaula. (UOL, via Mirror)
Dan wasan Atletico Madrid, Joao Felix, wanda ke taka leda aro a Chelsea na fatan kungiyar Stamford Bridge za ta saye shi. (Fijaches - in Spanish)
Arsenal ta fara tattaunawa da dan kwallon tawagar Faransa, Williams Saliba, domin tsawaita kwantiraginsa a Gunners. (Football Insider)
Al Nassr ta tnntubi wakilan dan kwallon Paris St-Germain, Sergio Ramos kan batun komawa Saudia da taka leda a badi. (Marca - in Spanish)
Dan wasan Inter Milan, Nicolo Barella na cikin wadanda Liverpool ke son dauka a kakar badi. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Liverpool na son daukar dan kwallon Bayern Munich da tawagar Netherlands, Ryan Gravenberch, wanda take fatan yake taka leda tare da dan wasan Ingila mai taka leda a Borussia Dortmund, Jude Bellingham. (Express)
Mai kungiyar Chelsea, Todd Boehly na duba yiwuwar sayen kungiyar da ke buga Ligue 1, Strasbourg. (L'Equipe)
Liverpool da Newcastle da Tottenham da kuma West Ham suna daga cikin kungiyoyin Premier League, wajen daukar dan kwallon Jamus, mai taka leda a Mainz, Anton Stach, mai shekara 24. (90min)
Dan kwallon Faransa, Marcus Thuram, wanda kwantiraginsa zai kare a bana a Borussia Monchengladbach, an tuntubi Barcelona ko za ta dauki dan kwallon, ana kuma alakanta shi da cewar zai koma Atletico Madrid ko Chelsea ko Inter Milan ko Manchester United ko kuma PSG . (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan da Newcastle ke son dauka Matheus Franca ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya da Flamengo, wadda ba ta amince da tayin da Newcastle ta yi ba na fam miliyan 17.5 a watan Janairu tun farko. (Sun)
Fulham da Everton da Leicester da kuma West Ham na rige-rigen daukar dan wasan Roma, Chris Smalling, mai shekara 33. (90min)
Newcastle United na son daukar dan wasa a karshen kakar nan wato dan kwallon Wolves', Max Kilman. (Football Insider)
LA Galaxy na son daukar dan wasan Chelsea, Andrey Santos, mai shekara 18, wanda bai samu zuwa buga wasannin aro a Palmeiras. (Goal)
Watakila Brazil ta dauki tsohon kocin Sifaniya da Barcelona, Luis Enrique, domin ya maye gurbin Tite, bayan da ake radi-radin za ta dauki mai horar da Real Madrid, Carlo Ancelotti. (Fijaches - in Spanish)
Dan kwallon tawagar Portugal, Nuno Tavares, mai shekara 23 ya ce zai koma Arsenal a karshen kakar nan da zarar ya kammala wasannin aro a Marseille (Goal)