Type Here to Get Search Results !

Ads

PSG ta zargi Chelsea da toshe zuwan Ziyech Paris

Top Post Ad

 

PSG ta zargi Chelsea da toshe zuwan Ziyech Paris



Dan wasan gefen Chelsea Hakim Ziyech na cikin yan wasan da yarjejeniyarsu ta lalace biyo bayan rufe kasuwar yan kwallo.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa LFP ta toshe batun zuwan nasa, a dalilin gaza kammala cika takardu a bangaren kungiyarsa Chelsea.

Rahotanni sun ce an cimma yarjejeniya kafinn cikar lokaci a Paris.

Sai dai wata majiya a PSG ta soki Chelsea da kin aikewa da takardun yarjejeniyar cikin lokaci har aka rufe.

Tuni ma har Ziyech ya isa birnin Paris yana jiran a tabbatar da yarjejeniyar amma hakan bata yiwu ba.

Saboda haka ba shi da zabi illa ya dawo kungiyarsa Chelsea, ya cigaba da wasa har zuwa karshe kaka.

BBC ta fahimci cewa dan wasan ya kira mai kungiyar Todd Boehly kai tsaye a kokarin ganin cewa cinikin ya fada, to amma duk da haka hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Ziyech ne dan wasa na farko da Chelsea ta saya tun bayan dage mata takunkumin sayen yan wasa a 2020, inda suka dauko shi daga Ajax kan fam miliyan 33.

Chelsea ta sayi Mykhailo Mudryk, David Datro Fofana, Noni Madueke da Joao Felix a wannan watan, baya ga Raheem Sterling da ta saye kafin a fara kaka.


Below Post Ad

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Listen Freedom Radio Live (PRO)

Freedom Radio Kano 99.5 FM

Freedom Radio Kaduna 92.9 FM

Freedom Radio Dutse 99.5 FM

Dala FM Kano 88.5

Hollywood Movies